Yadda amarya zata zabi kawayen ta watto bridesmaids

0
324

Shirye-shiryen biki yana da matukar wahala da gajiyarwa, amma zabar kawar ki a matsayin ki na amaryar babu gajiyarwa. Da zarar kin bayyana cewa an sa ranar auren ki a dandalin sada zumunta na yanar gizo, kawayenki zasu fara yin maki tambayoyi kamar haka, “wane kala za ki zabar wa ‘yan matan amaren ki? ” … “Don Allah kar a debo jan satin don bai dace da launin fata na ba!” Ko, “Ina fata ankon yan kawayen amarya ba za su yi tsada ba !” Da sauransu .
Hakanan zaki samu kira da yawa daga kawayenki suna son sanin ko suna cikin jerin yan matan amare.


’Yan matan amare watto kawayen amarya su ne za su kasance waɗanda amarya zata dogara da su don samun tallafi a duk lokacin da take buƙatan kuma sune zaki yi amfani da basirarsu yayin da kike shirin bikin auren ki.

Abubuwa da zaki yi la’akari da su wajan zaban kawayen ki sune.

Ajiye Rikod: komin tsawon lokacin da kika san kawarki ko danginki, ya kamata ki san wani irin mutune ne su, wanda ke da amfani yayin tantance yadda za su gudanar da ayyukan da ake tsammanin kawayen amarya suyi kafin da kuma lokacin bikin auren ki.


Kawaye da zaki amince da kuma ki dogara da: dogaro yana nufin za ki iya yin barci da daddare da sanin cewa cikakken aikin da kika sanya wa kowace kawayen ki za a yi. Dole ne ki tuna cewa amincewa da yan matan amaren ki don kula da wasu abubuwa don kada ki damu da abubuwan da ba su da mahimmanci yana da muhimmanci wajen rage maki aiyuka.


Kawaye da zasu tabbatar komai na Ƙarƙashin kulawa: kina buƙatar ƴan matan amaren ki su kasance waenda zasu tsaya maki. Ki Guji waenda suke kiran kansu divas waɗanda za su buƙaci ki ki shiga tsakani da kowane shawara, ɗawainiya ko aiki da za’ayi a wajan bikin ki.


Ki tabatar da cewa kuna da ajanda iri ɗaya: samun kawa mai kyakkyawar manufa a gefenki wanda ke da mafi ra’ayin ki a zuciyar ta kuma a ƙarshe ajanda iri ɗaya da ke; da sanin cewa wannan rana ce ta bikin sadaukarwar ki kuma ranar farin ciki ne, kuma rana ce da kike bukatar kawa da zata tabbatar da cewa komai ya je dai dai a lokacin bikin naki.

Kawar amarya ko Baƙuwa: Yana da mahimmanci ki lura cewa ba duk kawayen ki ba ne za su so su kasance cikin ƴan matan amaren ki ba. Don haka yana da matukar muhimmanci ki fara tamabaya ko tana ra’ayin kasancewa cikin jerin kawayen amarya ko kuma ta fi son halartan bikin a matsayin baƙuwa.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho