Yadda ake Hadda Meat Potatoe Balls

0
588

Abubuwan Bukata Sune:

  • Dankalin turawa
  • Nikakken nama
  • Attaruhu
  • Thyme
  • Curry
  • Tafarnuwa
  • Citta
  • Sinadarin dandano
  • Gishiri
  • Man gyada
  • Albasa

Yadda Ake Hadawa

  1. Da farko zamu fere dankalin mu,sai mu zuba acikin tukunya, mu sa gishiri da ruwa mu dafa.
  2. A wani tukunyan suya daban, mu sa man gyadan mu idan yayyi zafi sai mu zuba albasa da nikakken naman mu.             
  3. Bayan mun sa naman mu sai muyi ta juyawa har sai yayyi kalar dahuwa sai mu sa nikakken attaruhu,curry, thyme,citta da tafarnuwa mu juya.
  4. Sai mu sa sinadarin dandanon, mu juya har sai ya dahu.
  5. Bayan naman mu ya dahu sai mu dauko dafaffen dankalin mu, mu murmusa watto mashing in shi.                                                     
  6. Mu zuba naman, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin dandano,curry, thyme a cikin dankalin mu juya su hadu.
  7. ki shafa man gyada a hannun, sai ki dibo hadin dankalin sai ki mulmula.
  8. Bayan kin gama mulmulawa, ki fasa kwai a wani kwanu daban sai ki sa man suyan ki a wuta yayyi zafi.                                           
  9. Idan man ki yayyi zafi sai ki dauko dankalin kid a kika mulmula ki sa a cikin kwai sai ki jefa a cikin man kid a yayyi zafi.
  10. Haka zaki yi har sai kin gama soya duka dankalinki.
  11. Meat potatoe balls ya hadu a ci lafiya.

 

Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho