Duk wanda ya kira ni kan ci gaban Kannywood zan je – Naburaska

0
217

Fitaccen Jarumin masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannaywood Mustapha Badamasi wadda akafi sani da Naburaska ya ce, duk dan siyasar da ya kira su domin tattaunawa kan ci gaban sana’ar su kai tsaye za su je wurin sa babu duba jam’iyyar da ya fito.

Jarumin ya bayyana cewa, Duk da cewar yana jam’iyyar PDP tsagin Kwankwasiyya, idan har Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kira shi domin baiwa Kannywood ci gaba kai tsaye zai je wurin sa, amma hakan ba ya na nufin yabar jam’iyyar da yake ciki ba ne.

Ya kara da cewa, Ganin sa tare da gwamnan jihar Sakoto Aminu Waziri ba zai taba masa siyasar sa da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Inji Naburaska.Naburaska.

 ya kuma kara da cewar, shugabannin hukumar tace fina-finan hausa na lokacin mulkin Ganduje sun gaza wajen ci gaban sana’ar, a daidai wannan lokacin da kasuwancin ta ya durkushe. Ya fadi hakan ne a hirar da rediyon dala tayi da shi.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho