Yan Najeriya hudu Da Suke rike Da Manyan Mukamai A Duniya

0
116

 

Najeriya kasa ce da ake girmamawa sosai a fadin duniya.  Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi yawan jama’a a duniya baki daya.  Najeriya ta samar da manyan mutane maza da mata tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kai daga kasar Britaniya a shekarar 1960. A yau zamu leka zuwa ga wasu ‘yan Najeriya da ke rike da manyan mukamai a duniya.

 

  1. Amina Mohammed

A halin yanzu Hajiya Amina Muhammed tana da shekaru 60 a duniya.  A halin yanzu  tana rike da babban mukami a Majalisar Dinkin Duniya.  Ita ce mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai ci.  Ta kuma rike mukamin ministar muhalli a Najeriya.

 

 

  1. Ngozi Okonjo-Iweala

Madam Ngozi-na daya daga cikin mata masu fada a ji a Tarayyar Najeriya.  Ita ce babbar Daraktar Hukumar Kasuwanci ta Duniya a halin yanzu.  Ita ce bakar fata ta farko da ta rike wannan mukamin.

 

  1. Akinwumi Adesina

A halin yanzu Akinwumi Adesina yana rike da mukamin shugaban bankin raya kasashen Afirka.  Akinwumi Adesina ya kuma taba rike mukamin ministan noma a tarayyar Najeriya.  A halin yanzu yana da shekaru 62 a duniya.

 

  1. H.E.  Dakta Hajo Sani, OON

Dokta Hajo Sani kwararriya ce ta ilimi kuma manazarci wacce ta shafe shekaru da dama tana gogewa a harkar koyarwa da gudanar da harkokin gwamnati.  Ta yi Digiri na farko a fannin Ilimi, Digiri na biyu a fannin Guidance da Counseling da Digiri na uku a fannin Gudanarwa da Nazarin Siyasa.  Ta kasance shugabar makaranta na tsawon shekaru goma sha biyu kafin a nada ta a matsayin ministar harkokin mata da ci gaban zamantakewa ta tarayya (1997-98).  A lokacin da take rike da mukamin, ta jagoranci wata tawaga zuwa Majalisar Dinkin Duniya (UN) tare da kare rahoton kasa na 2 da na 3 kan CEDAW a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 19 a birnin New York.  Dr. Sani ta taba zama Sakatare-Janar na Kungiyar Mata ta Yammacin Afirka (WAWA), reshen Najeriya, daga 2000 – 01.

A shekarar 2021, gwamnatin tarayyar Najeriya ta nada Dr. Hajo Sani a matsayin Jakadiyar Dindindin Dindindin na Najeriya a UNESCO a birnin Paris na kasar Faransa.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho