‘Ya’yan Itatuwa Don Gyara Gashi!

0
136

 

Gashi mara sheki, lalacewa da tsinkewa matsala ce ta gama gari ga mata daban-daban. Damuwa, yanayin lokaci na hunturu da ma sauran su na jawo lalacewan gashi, lafiyar gashi ya danganci abin da ake amfani da su akan gashi ko ci.

Ana bukatan abubuwa da suka dace a yi amfani da su a gashi don turarawa a gashi wato steaming don gyara na musamman a gida ba tare da kin je wajen gyaran gashi ba wato saloon.

Akwai kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa da yawa don habaka gashi wadanda mata da dama basu sani ba – cin wandannan kayan itatuwan da amfani da su a gashi zai kawo babban canji a lafiyar gashi.

‘Ya’yan itace sune tushen bitamin da sauran sinadarai ma su gina jiki da lafiyan gashi don bitamin da fiber na da mahimmanci ga lafiyan gashi.

Jerin ‘Ya’yan Itatuwa Guda Bakwai Da Yadda Za’a Yi Amfani Don Habaka Gashi

●Guzberi (Gooseberries Amla) : Ana samun man Amla a shafa a gashi don kara sheki da cika. Yana kuma rage furfura wato gray hair.

●Strawberries: Sami strawberries kwara 5 zuwa 10, ki nika sai ki shafa a gashi bayan kin wanke. Za ki iya hada su da abun turara gashi na kanti (hair Mayonnaise )

●Lemu (Oranges ): A matse ruwan lemu biyu, sai a shafa and tausa gashi sosai. A bar shi na tsawon minti 30 zuwa awa daya sai a wanke da ruwa mai dumi.

●Ayaba: Nika ayaba guda daya ko biyu, za’a iya hadawa da zuma, a shafa sai a rufe da leda na minti 30 sai a Wankegashi da ruwan dumi.

●Apples: A fitar da ruwan cikin sa Sai a shafa a gashi baki daya na minti 30. A dauraye gashi da kyau.

●Gauva: A sami wanda ya nuna sosai, a nika sai a shafa a gashi – zaa iya diga masa zuma ko mayukan mai (essential oils). A wanke bayan minti 30 zuwa awa daya.

●Gwanda (papaya): A samo nunanen gwanda, a nika sai a hada da man mayuka da ya dace da irin gashin ki sai a shafa na minti 30, a wanke bayan nan da ruwan dumi.

 

Daga Safrat Gani