Yusuf Buhari zai angonce da ‘yar Sarkin Bichi,

0
449

Da namiji tilo guda daya ga shugaban kasan nijeriya Muhammadu Buhari watto Yusuf Buhari,  na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, kamar yadd muka samu rahoto daga Daily Nigerian. Zahra Bayero yanzu haka daliba ce a kasar birtaniya kuma tana  karatun ilmin zanen gine-gine a kasar, yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami’ar Surrey, Guildford, a Birtaniya. Majiyoyi sun bayyana cewa za’a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa. “An kaddamar da shirye-shiryen bikin. Kamar da al’ada ta tanada, iyayen mijin sun kai gaisuwa wajen iyayen Zahra,” cewar majiyar da aka sakaye sunanta. Majiyar ta kara da cewa da tuni an yi bikin amma saboda rashin kasancewar mahaifiyar Yusuf, hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo daga Dubai inda ta kwashe watanni shida. “Tun da yanzu a dawo ana gab da azumi, lallai za’a yi daurin auren bayan Sallah,” majiyar ta kara.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho