Kurakurai guda 4 da ya kamata ku guji tafkawa a matsayinku na masu amfani da gas cooker

0
604

Gas Cookers na ɗaya daga cikin hanyoyin da yawancin mutane ke amfani da wajen girka abincinsu. Saboda yana da sauƙi da sauri fiye da yawancin hanyoyin dafa abinci.
Wannan kadan ne daga cikin fa’idodin da ke zuwa tare da yin amfani da  gas cooker amma kamar sauran abubuwa, gas cooker shima yana da wasu illoli amma ana iya sarrafa shi da kyau tare da sanin kuskuren da ke haifar da shi ilolin.

 Ayau, za mu yi magana akan kurakurai 4 da kan iya haifar da matsalar fashewar iskar gas da ya kamata ku sani

 1. Yin amfani da burner mara kyau
A matsayinka na mai amfani da tukunyar gas, kuskure ɗaya da ya zama ruwan dare gama gari da ya kamata ku daina shine yin  amfani da burner mara kyau.  An tabbatar da hakan na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da fashewar tukunyar gas a mafi yawan wuraren da ya faru.

 A mafi yawan lokuta, yawanci ana samun fitowan iskar gas daga wannan burner da bashi da kyau wanda hakan yake da haɗari sosai.

 2. Cika silindar gas ɗin ku har zuwa  baki

 Wannan wani kuskure ne da ya kamata ku daina yi.  Cika silinda da iskar gas har baki zai iya haifar da zubar  iskar gas daga silinda wanda kan iya jefa ku cikin hadarin fashewar gas.

 Madadin haka idan silinda gas ɗinka silinda ce mai nauyin kilogiram 10, kawai siyan iskar gas ɗin kilogiram 9.5 don hana cikawa ga baki ɗaya.

 3. Barin yaranku suyi amfani da gas cooker

Kuskure ne ku ƙyale yaranku suyi amfani da t gas cooker musamman kanana. Saboda ƙila yaran ba  su san matakin da za su ɗauka ba idan wani rikici ya faru yayin da suke amfani da gas cooker in.

 Zai fi kyau ku yi amfani da tukunyar gas da kanku ko ku ƙyale yaran ku kawai suyi amfani da su lokacin da suka girma.

 4. Yin amfani da silinda mai tsatsa

 cylinder Mai tsatsa yawanci yana haifar da zubewar iskar gas.  Wannan shi ne saboda mafi yawan waɗannan silinda gas lokacin da suka yi tsatsa suna da ƙananan ramuka waɗanda zasu iya saki wani nau’i na iskar gas wanda zai iya haifar da fashewar gas.
By: Firdausi Musa Dantsoho