Amfanin man kadanya guda 10 ga Fatar jikin mu

0
1804

Man kadanya watto  Shea butter yana da fa’idodi masu yawa ga fata.

 Ana samun man kadanya  ne daga ’ya’yan itacen kadanya da ake nomawa a yammacin Afirka.  Yawancin lokaci yana da ƙarfi kuma yana kama da kirim ko fari.

 Man kadanya yana da amfani ga kowane bangare na jikin mu.

 Yana da fa’idodi marasa Misali saboda yana ɗauke da sinadarin bitamin A, E, da F, linoleic, palmitic, stearic, da oleic fatty acid da ma sauran sinadarai.

 An tabbatar da cewa man kadanya  yana magance ciwon mahadin kashi da kumburi. Abin da kuke buƙata shine shafa shi akan wajan da abin ya shafa.

 Eczema, dermatitis, da psoriasis na iya haifar da kaikayi da kumburi.  Shafa man kadanya a wurin da abin ya shafa na iya rage yiyuwan haka.

 Ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da amotsanin shine bushewar kai.  Man kadanya yana rage bushewar gashi ta hanyar samar da danshin da ake bukata.

Man kadanya  ya ƙunshi triterpenes waɗanda ke taimakawa haɓaka samar da collagen wanda ke ƙarfafa fata kuma yana hana yamutsewan.

Yawan maiko na iya haifar da Kuraje da pimples.  Yin amfani da man kadanya a fata yana taimakawa wajen daidaita samar da mai.  Sinadarin antibacterial da yaƙe da shi na kashe kwayoyin cuta kuma yana hana pimples.

 Bincike ya nuna cewa man kadanya na shea butter yana hana keloid fibroblasts wanda ke haifar da tabo da kuma stretch marks daga fitowa a fata da kuma  yana hana tabo da kuma stretch marks.

 Idan kuna fama da zubewar gashi.Toh a rika amfani da man kadanya domin  hana zubar gashi.

 Shafa man kadanya na sa raunukan su warke kuma yana rage bayyanar tabo da ja da kumburin da kwari ke haifarwa.

 Yin amfani da man kadanya a hanci zai rage cunkoson hanci.

Wannan shine mafi yawan amfani da man kadanya ke da shi ga fatan mu.  Yana sa fata ta yi laushi da sheki.

By: Firdausi Musa Dantsoho