Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

0
672

Allah Ya yi wa fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth rasuwa. Zainab Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

Jaruma Maryam Booth ce ta sanar da rasuwar mahaifiyar tata a shafinta  na Instagaram.

Mabiya shafinta na  Instagram da abokanayan sana’anta na Kannywood da nollywood sun yi tururuwa wajen aika sakon ta’aziyya da jaje ga jaruman da iyalanta.

A ranar Juma’a 2 ga watan Yuli ne aka yi jana’izar tauraruwan wasan kwaikwayo na hausa, Zainab Booth, wacce ta rasu a ranar Alhamis, a birnin Kano aka birne marigayiyar wacce ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

Daruruwan abokan aikinta da masu aiki a masana’antar fim, irin su Ali Nuhu, Falulu Dorayi da Yakubu Mohammed da masoya da dama sun hallarci jana’izar. Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Domin tunawa da marigayiyar jarumar, jaruman Kannywood maza da mata da dama sun wallafa hotunanta a shafukansu na sada zumunta. Dan uwanta, Ramadan Booth, shima ya yi addu’ar Allah ya jikarta da rahama ya gafarta mata. Marigayiya Booth ta rasu ta bar yara hudu; biyu maza da biyu mata.

Marubuciya:Firdausi Musa Dantsoho