Jarumin Bollywood Aamir Khan da matarsa Rao sun rabu bayan shekaru 15 da aure

0
248

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Amir Khan ya sanar a ranar asabar uku ga watan yuni da cewa zai rabu da matar sa da suka yi shekara 15 da aure watto mai shirya fim Kiran Rao, kamar yadda `The Guardian ta ruwaito.  ma’auratan sun sanar da rabuwar su amma sun yarda zasu ci gaba da kula da dan su kuma zasu ci gaba da wasu ayyukan tare.

Sun bayyana  cewa : “A tsawon shekaru goma sha biyar [15] da muka shafe tare mun karu da juna sosai yayyin tafiyar da rayuwan mu cikin walwala da raha, kuma alakar mu ta ginu cikin aminci, girmamawa da kaunar juna.” “Yanzu muna bukatar bude sabon shafi a rayuwar mu — amma ba a matsayin mata da miji ba, sai dai matsayin iyaye da kuma iyali ga kowannen mu.”

 Khan da Rao sun hadu ne lokacin daukar wani fim a shekarar 2001 kuma Rao ce mai taimakawa mai bada umarni, kuma suka yi aure a watan Disambar 2005. Jarumin mai shekaru 56, wanda fim dinsa na dambe, ‘Dangal’ ya maida shi babban tauraro a kasar China, sun rabu da matarsa jaruma Reena Dutta a 2002.

Ma’auratan sun ce”Mun fara shirye shiryen rabuwa wasu lokuta, amma yanzu ne muka ga dacewan mu zartar da wannan hukunci, na rayuwa ba a tare da juna ba, amma zamu cigaba da gudanar da rayuwa yadda ta kamata tare,” Khan da Rao suka ce.

“Zamu kasance iyayen masu kula da dan mu Azad, wanda zamu raina kuma ya tashi a hannun mu. Za kuma mu ci gaba da aikin hadin gwiwa a fim, gidauniyar Paani da sauran ayyukan da muke da sha’awa.” Khan da Rao yar shekara 47, sun godewa yan uwa da abokan arziki “wanda a cewan su da babu su baza su iya yanke hukunci cikin salama ba.” “Muna rokon masu fatan alheri da su yi mana fata na gari, kuma tare da fatan za su gane ba mun rabu ne har abada ba, hanya ce ta fara sabuwar rayuwa.”

Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho