Allah Yayiwa Babban Mawaki Sound Sultan Rasuwa.

0
46

‘Yan Nigeria na cike da alhinin rasuwar babban mawakin turanci da yaren yarbawa, Olanrewaju Ganiu Fasasi wanda aka fi sani da sound sultan

Mawakin ya rasu ne a ranar lahadi 11, ga watan yulin 2021 sanadiyar cutar kansa mai suna angioimmunoblastic t-cell lymphoma kamar yadda yayansa Dr. Kayode Fasasi ya wallafa a wata sanarwa daya fitar a ranar lahadin sanadiyar rasuwar qaninsa din.

Mawakin ya rasu yana da shekaru 44 kuma yabar mata daya da yara uku da yan uwansa maza da mata. Muna fatan Allah yayi masa rahmah.

Daga Maryam Idris

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here