Fitacciyar mai wakokin yabon annabi sayyada Rabi’atu Harun ta rigamu gidan gaskiya,ta rasu ne a jiya talata 16 ga watan maris shekara ta 2021 a rigasa kaduna.
Mijin marigayyiyan sharif mu’az ne ya tabbatar da rasuwarta yayyin da ya bayyana cewa ta rasu ne bayan jinya na makonni uku, ya kara da cewa mutuwarta ta girgiza shi ya bayyana matarsa a matsayin mace mai hali nagari ya kara da yin mata addu’ar Allah ya jikanta da rahama.
Marigayyiyan ta yi wakokin yabon manzon Allah masu tarin yawa ciki akwai mai daraja annabi ma’aiki, zahra’u fadima,shukriyya sajida da sauransu masu son wakokinta sunyi jimamamin rasuwarta tare da yin mata adu’an Allah ya jikanta ya gafarta mata.
Ta rasu ta bar mijinta da ya’ya biyu a duniya, allah ya jikanta da rahama amin.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho