Tsohuwar jarumaMansur Isah Tayiwa Gwamantin Nigeria Martani Mai Zafi Kan Sace Dalibai

0
365

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mata ga fittaccen jarumi kuma mawaki san musa danja watto Mansurah Isah ta bayyana bakin cikinta  kan yanda aka rasa nuna halin damuwa da sace dalibai da akayi a Arewa.

Ta tambayi cewa shin ‘yan Legas ne kadai zasu iya yakar gwamnatin Najeriya da kawo Canji, saboda Su kadai gwamnati take jin tsoro.

Tace suna fitowa su bayyana damuwarsu ba tare da fargaba ba, kuma kana taba daya daga cikinsu kamar ka taba dukansu ne, basa yacewa juna baya.

Tace babu Munafurci ba Kyashi ba bakin ciki. Tace ana magana yanzu, ko wani abune ya sameka, musulmi dan uwanka ne zai fara cewa Allah kara, kadan ma ya gani, Allah kara mishi Musiba. Tace da sune aka sace yara a Makaranta, ai da yanzu sun hana gwamnati bacci, da sun ta yayata abin a shafukan sada zumunta ta yanda kasar Amurka tuni zata shiga maganar.

Mansurah ta bayyana cewa gaskiya tana cikin damuwa sosai kan wannan lamari. Ta kara da cewa, yanzu maganar ‘yan fim ce kawai zata sa a hade kai ai ta cece-kuce akanta.

Mansurah tace bafa wanda zai taimakemu sai mun tashi mun taimaki kanmu. Tace tana kira da a fito a yi magana kan matsalolin Arewa.

Ta  wallafa hakan ne a shafinta na  Instagram .

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho