Guinea-Bissau ta yi alfaharin kawo karshen rawar da Super eagles ta taka a wasan AFCON 2021 a baya.

0
93

 

Yan wasa da jami’an kasar Guinea-Bissau sun yi alkawarin kawo karshen gasar da Najeriya ta yi ba tare da an doke su ba a yau a wasansu na karshe na rukuni a birnin Garoua.

Eagles ce ke kan gaba a rukunin da maki shida, yayin da Guinea Bissau ke matsayi na uku da maki daya. Wasan na yau zai gudana ne da karfe 8.00 na dare.

Guinea Bissau ta yi kunnen doki 0-0 da Sudan a wasansu na farko, inda suka yi rashin nasara a bugun fanariti da aka ba su a karshen wasan, sannan suka fado a hannun Mohamed Salah a wasansu na biyu na rukuni, wanda har yanzu suke ganin sun ci kwallo mai kyau, amma aka soke.

Da yake magana jiya, dan wasan tsakiya na Guinea Bissau, Panuche Camara, ya bayyana shirinsu na dakatar da Super Eagles a wasan na yau, yana mai cewa: “Ina da kwarin gwiwa cewa za mu yi nasara akan Najeriya gobe (yau). Na san cewa Super Eagles na yin faretin manyan ‘yan wasa a Turai, amma za mu daidaita su karfi da karfi.”

Ya kara da cewa Djurtus ba za ta sake tafka kuskuren da ya jawo ƙasar Masar tayi nasara akansu ba.

 Kocin, Baciro Cande, ya kuma bayyana cewa dole ne Super Eagles ta fadi. “Muna son mu tabbatar da cewa Guinea Bissau tana da ‘yan wasa nagari wadanda za su iya lashe kofin AFCON a nan Kamaru.”

By: Firdausi Musa Dantsoho