An samu cunkoson Ababen hawa na sama da awanni 5 a babban titin maraba

0
61

An samu cunkoso ababen hawa akan babbar hanyar zirga-zirga a  Mararaba – Nyanyan a babban birnin tarayya (FCT) da motoci, babura, da masu tafiya a kafa suka makale na sa’o’i da dama,a sanadiyar faduwar wata babbar doguwar motar daukar kaya wato trailer.

An gano cewa, kulle-kullen wanda ya faro ne da misalin karfe 5 na safiyar yau Alhamis, ya faru ne sakamakon wata tirela mai dauke da tarkacen karfe, wadda ta fado kai tsaye a kan babbar hanyar da ta doshi tsakiyar birnin, kusa da Barikin Abacha, lamarin da ya sanya masu ababen hawa suka sako motocin su ta hanyar da bata dace ba inda hakan ya kawo gagarumin cunkoso.

An ga fasinja suna saukowa daga cikin motocin bas don fara tattaki da ƙafa zuwa mashigar AYA, yayin da wasu ke hawa  babura.

A sakamakon kulle-kullen da aka yi, masu tuka babur suna karbar Naira 1000 daga Nyanyan zuwa AYA, yayin da daga Kugbo kuma suke karbar Naira 700 zuwa N500 zuwa AYA.

An ga mahayan babur suna amfani da magudanun ruwa a matsayin hanyoyin da za su haɗa zuwa zagayen AYA saboda toshewar hanyar.

Masu tafiya a ƙasa da masu ababen hawa sun zargi hukuma da barin tirelar da kayanta su ci gaba da kasancewa a kan titin har zuwa safiya, lamarin da ya haifar da kulle-kullen da ba a kula da shi ba a daya daga cikin manyan hanyoyin mota a yankin.

An ga hadaddiyar tawagar ‘yan sandan Najeriya, da kiyaye hadurra, da na Civil Defence ke  kokarin shawo kan cunkoson ababen hawa tare da kwashe tarkacen tirelolin da ke kan titin.

Daga Fatima Abubakar