Da, mahukunta sun shigo harkokin fina-finai da an gyara duk wata barna a masana’antar inji  Aminu Saira

0
302

Fittaccen mai shirya fina-finan Hausa ta Kannywood  watto Malam Aminu Saira,  ya bayyana cewa, idan har ana son a gyara harkokin fina-finai to wajibi ne sai malamai da kuma al’umma sun shigo cikin lamarin domin samun gyaran da ya dace.

Aminu Saira ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Freedom Radio, yana mai cewa yadda mutane suka yi watsi da lamarin fina-finan Hausa ne ya sanya a ke samun matsalolin da ake gani a yanzu a kamfanin.

A cewarsa mai shirya fina finan“Da mahukunta sun shigo cikin harkokin shirya fina-finai da zuwa yanzu an gyara duk wata barna da ake ganin ana yi a cikin masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.”

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho