Tayi sujjadar godiya ga Allah bayan da ta gan Ni inji mawaki Nura M Inuwa

0
1430

Shahharraren mawaki, wadda yayyi fice a kamfanin shirya fina finai ta Kannywood, haka zalika, ya kasance mai dumbim masoya kuma ana ganin wakansa a matsayin nasiha ba,a iya nan ba, wakokinsa ya gyara zamantakewan aure inji wasu  watto mawaki  Nura M Inuwa ya bayyana  yadda wata masoyiyarsa tayi sujjudul shukhur yayyin da tayi ido biyu da shi.

Matashiya wadda Sunan ta  Hafsat ne  amman a yanzu ana kiran ta da Nuriyya saboda tsananin kaunar da take yi wa mawaki Nura M Inuwa.

A ranar Lahadi ne Nuriyya tayi sujjadar godiya ga Allah bayan da aka hada ta da mawaki Nura M Inuwa

Nura M inuwa ya bayyana hakan ne a shafin sada zumuntan sa na facebook,  inda muka samu labarin. Mawakin  ya wallafa rubutu haka yake cewa “

 “Hafsa take, amma ana kiranta da Nuriyya dalilin son da take mini,data ganni tayi sujjadar godiya ga ubangiji, ta zubar da hawayen da suka kashen min jiki, a karshe ina rokon Allah ya azurtata da muji nagari.”

Wannan abun yayyi wa masoyan mawakin daddi yayyin da suka ta yabonsa, haka zalika, kamar yadda muka sanni yayyin da wasu ke yabon jarumai wasu kuma na sukar su haka ma ga mawakin wasu sun soke shi gamme da sujjadar da matashiyan tayi.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho