Darakta Hassan Giggs da matarsa Muhibbat Abdulsalam sun cika shekaru goma sha uku da aure

0
363

Fittaccen darakta a kamfanin shirya fina-finan hausa ta Kannywood Hassan  Giggs da matarsa tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdulsalam sun cika shekaru goma sha uku cif da aure.

Daraktan da matarsa sun kasance cikin jaruman Kannywood da suka aura juna, kuma auren yayyi karko, banda haka sun kasance ma’aurata masu son ganin cigaban juna da kuma taimakawa juna.

Hassan Giggs da muhibbat cike da farin ciki, sun sanar cikan su shekaru goma sha uku da aure  a shafinsu na Instagram.

Darakta Hassan ya fara da godiya ga Allah (S.W.T) ubangijin talikai sama da kasa, dan adam da aljannu da mala’iku da komai da komai daya nuna masu shekara goma sha ukku 13 da aure.

Ya kuma gode wa ubangiji da ya hada shi da kyakyawan matarsa,kuma uwar kyawawan iyayansa Humaira,Azeema da khadija.

Itama muhibbat kamar yadda ta wallafa a shafinta ta fara ne da godiya ga ubangiji,tare da bayyana cewa yau auren su shekaru goma sha uku tare da Hassan Giggs, sa’annan tayi fatan Allah ya kara masu so da kaunar juna ya raya masu zuri’an su ya kuma sa Hassan ne mijinta a aljanna.

Manajan Tozali da  ma’aikatan ta na tayasu murna tare da yin masu fatan alkhairy.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here