Fittacen Mawaki Mai Tasowa Namenj Ya Saki Waka Mai Taken DAMA Tare Da Mawaki Mai Tashe Hamisu Breaker

0
326

Hazikin mawaki kuma marubucin Arewa Afropop da Afrobeat Ali Jubril Namanjo wanda akafi sanni da suna namenj sun hada kai da mawaki mai tashe hamisu breaker a cikin wata sabuwar waka mai taken DAMA.

Wakan da aka sake ta a ranar juma’a biyar ga watan maris, shekara ta 2021 ya samu karbuwa sosai domin kuwa fitattun jarumai da mawaka sun sanya wakan a shafinsu na yanar gizo.

Haka zalika ayau 8 ga watan maris shekara ta 2021 da rana  wakan shine na goma sha takwas a cikin wakoki  dake tashe a youtube.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho