Gwamnan Gombe Ya Naɗa Sabin Masu Bashi Shawara Na Musamman, Da Babban Darakta, da kuma Manyan Mataimaki Na Musamman 

0
6

Gwamnan Gombe Ya Naɗa Sabin Masu Bashi Shawara Na Musamman, Da Babban Darakta, da kuma Manyan Mataimaka Na Musamman

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da naɗin wassu muhimman mukamai don inganta harkokin gwamnatin jihar da zaburar da manufofinta na ci gaba.

Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya sanar da amincewar gwamnan, yana mai cewa sabbin naɗe-naɗen sun ƙunshi muhimman sassan da suka haɗa da tsaro, da bunƙasa jin daɗi da walwalan jama’a, da daidaiton jinsi, da bunƙasa damammakin ilimi, da harkokin gudanarwa, da bunƙasa sana’o’in fasaha.

Sabbin waɗanda aka naɗan sune: AIG Zubairu Mu’azu (Mai Ritaya), a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro; da Aishatu Adamu mai ba da shawara ta musamman kuma kodinetar shirin tallafawa jama’a; da Finney David, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin mata a ƙarƙashin shirin Nigeria for Women Project, da Amina Ɗahiru Usman Bauchi, mai ba da shawara ta musamman kan Almajiranci da harkokin Tsangaya.

Hakanan an naɗa: ACP Ibrahim Bappa (Mai Ritaya) a matsayin Babban Darakta kuma Kwamandan GOSTEC; da Ibrahim Saidu Umar, Babban Mataimaki na Musamman na (1) akan harkokin tsare-tsare wato Protocol Matters da Yakubu Sarma, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman na (1) kan manyan Ayyuka. Dukkanin naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

 

Hafsat Ibrahim