HAKIKA NA SABA MAKU AKAN RASHIN SANI, SAKO MAI RATSA ZUCIYA DAGA MAWAKI NURA M INUWA ZUWA GA MASOYANSA

0
443

Fittaccen mawakin Kannywood wadda ke tashe haka zalika akayi shekara ta 2020 ba tare da ya saki waka ba wadda hakan ya jawo zanga zanga  watto Nura M Inuwa ya wallafa sako mai ratsa zuciya ga masoyansa a kan dalilinsa na rashin fitar da faifen wakokinsa biyu da yayyi alkawarin fitarwa a karshen watan fabrairu, sai gashi an ji shi shiru.

Masoyan mawakin sun kagu su ji sabobin wakokinsa ne saboda mawakin ya dau lokaci mai tsawo bai fitar da wakansa ba.

Shahararren mawakin yayyi Magana da kalamai masu  hikima ga masoyansa a shafin nasa na Instagram inda yace”hakika na saba maku akan rashin sani, na kuma fahimci shiru bazata gamsar da kuba,na so ace shirun da nayi yazo da waraka tun kafin ku magantu, sai dai kuma kash bani da iko a hannu, ku kuma kaguwa ta hanaku zuban ido,wannan sai ya dada fahimtar dani tabbas ba komai zaka so ka samu ba a lokacin da kake so ba, da ni da ku baza mu iya kauda abun da Allah yake son gani ba,amma a karshe ina neman afuwanku ku yafe min Dan Allah . kamar yadda na fada nayi nawa Allah yayyi mini nasa, kuma nasan nan dka mun sanni shine dai dai, a karshen ina mai dada baku hakuri, nasan tunda  ku kayi  hakuri a baya mai yawa insha Allah gajeriya gaba ma baza ta gagareku ba nagode assalamu alaikum.

Tabbas duk wadda suka cika masoyan wannan mawakin bazasu ki yin mai afuwa ba da irin waenan kalamai masu ratsa zuciya da yayyi masu.

A karshe de muna fatan Allah ya bashi ikon fitar da faifen wakokinsa a sa’a .

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho