HANYOYI SHIDA DA ZAMUBI DON GYARAN FATAN JIKIN MU 

0
129

 

Fatar jikin mu nada matukar amfani a gare mu, mu rinka gyarawa. Hanyoyi shida da zamubi don gyaran fatar jikin namu.

  1. Na farko, zaki samu garin bawon lemu wanda aka busar, sannan ki daka ki tankade sai ki hada da baking soda ki rinka shafawa na wasu mintina Kaman minti goma ko sha biyar kafun kiyi wanka yana magance cututukan fata.
  2. Na biyu, zaki hada ruwan lemun tsami dana zuma sannan ki shafa a fuska ko jiki,hakan zai inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje.
  3. Na uku, zaki samu man zaitun da madara ki kwaba sai ki shafa jikin ki dashi yayi minti goma ko ashirin sai ki wanke da ruwan dumi, yin hakan yana magance gautsin fata da kuma sanya fata taushi.
  4. Na hudu, zaki samu ayaba da ruwan lemun zaki da kuma kindirmu sai ki kwaba ki shafa a jiki, ki bari yayi mintuna sai ki wanke, yin hakan na magance tattarewar fata.
  5. Na biyar, zaki cire kwaiduwar cikin kwai da ayaba da man zaitun ki kwaba a wuri guda,sai ki shafa a jikinki ko a fuska na tsawon minti ashirin sannan ki wanke da ruwan dumi.
  6. Na shida, zaki kwaba madara da man zaitun sai ki shafa a fuska na tsawon mintuna sai ki wanke, yin hakan na magance gautsin fata da kuma sanya fata taushi.

Daga, Faiza A Gabdo