Ina tunanin tsayawa takara shekara ta 2023 – cewar Rukayya Dawayya

0
320

 

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta soma tunanin za ta shiga sahun masu neman wani mukami na siyasa, idan Allah ya kaimu lokacin zabe na shekarar 2023.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar ta da jaridar dimokuradiyya,dangane da rawar da ‘yan fim za su taka, a lokacin zabe mai zuwa, inda ta ke cewa “Na shiga siyasa a zaben da ya wuce na yi ta Kano na Jigawa da kuma jihata ta Katsina, domin a nan ma na fi bada karfi a siyasar, don Mahaifina dan Katsina ne, a wani kauye a Matazu, Mahaifiyata ita ce shuwa Arab, amma dai a Kano muke da zama sai dai, duk wasu takarduna na Katsina ne don haka ne, na fi bada karfi a siyasar Katsina “. Inji ta

jarumar ta cigaba da cewar” kuma Alhamdulillah, yanayin yadda muka gudanar da siyasar ya kara mini karfin gwiwa, kuma na gane cewar, lallai akwai sauran aiki a gaban mu, sabida duk wanda ya ke so ya yi wani yunkuri, wanda zai taimaka wa kansa, to dole ne sai ya zama ko’ina yana nan. Kuma na gane fitaccen mutum, wanda aka sani shi ne ya kamata ya shiga siyasa, saboda abu ne na sanin jama’a, don haka wannan siyasar da na shiga ya sa na samu wani karfin gwiwar da na ke tunanin zan iya fitowa takara idan aka zo lokacin zabe na gaba, kuma ina ji a jikina zan iya cin zaben a duk mukamin da na ne ma. ” A cewar ta.

Daga karshe Rukayya Dawayya ta yi kira ga abokan sana’ar ta da su San darajar da Allah ya yi musu ta farin Jini, kuma su san yadda za su kiyaye mutuncin su, da baiwar da Allah ya yi musu. Dawayya, ta soma tunanin ita za ta shiga sahun masu neman wani mukami na siyasa ne, idan Allah ya kaimu lokacin zabe na shekarar 2023.

Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here