Har yanzu ana ya yi na a masana’antar Kannywood inji jaruma Fati Bararoji

0
548

 


Tsohuwar jaruma fina-finai hausa ta Kannywood wadda har yanzu ake damawa da ita a masana’artan watto Fati Baffa Fagge, wacce a ke wa lakabi da Fati Bararoji, Ta bayyana cewar ita fa har yanzu ba ta yi tsufan da za a daina yayin ta ba a cikin masana’antar, domin kuwa, har yanzu a na damawa da ita kamar lokacin kuruciyar ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da tayi da jaridar Dimokuradiyya, dangane da har yanzu irin su da suka dade a harkar ba su bar wa yan baya ba, watto jarumai da suka shigo harkar a yanzu, kasancewar su jaruman da suka ci lokacin su a baya.

Sai dai Jarumar ta yi saurin bada amsa da cewar “Sam babu wani lokacin mu da za a ce mun ci a baya, kuma yanzu mun zo muna cin na wasu, domin babu wanda ya ke cin lokacin wani, don haka yanzu ma lokacin mu ne.” Inji ta.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba a fiye ganin ta ba sosai, sai ta ce “Ai da ba a gani na, ba Wai na daina fim ba ne, wasu harkokin kasuwancin da na ke yi ne, su ka sa ba a gani, don kada na karbi aikin mutane ya zama ban samu zuwa ba, Amma da ya ke a yanzu ina samun lokaci ai ga shi ana gani na, don haka babu wani-daina yayin mu da aka yi, kuma har yanzu muna cin lokacin mu ne.” Kamar yadda ta ce

Daga karshe ta yi kira da masoyan ta da su ci gaba da kallon fina-finan da za su fito nan gaba, domin za su ci gaba da ganin ta musamman fina-finan da a ke haskawa a gidajen talbijin manya, irin su Arewa 24 da sauran su.

Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho