KALMOMIN DA YA KAMATA SU KASANCE A BAKIN MASOYA A KODA YAUSHE.

0
620

 

Jimla ta kalmomi uku,”inasonka” ta wanzu shekaru aru aru, kuma ta karfafa dangantaka tsakanin masoya,masoya sun kasance suna amfani dashi akoda yaushe domin ci gaba da tabbatar da soyayya ga junansu,hakika ko ta yaya ne akwai wasu kalmomi wadanda zaku iya amfani dasu don bawa abokin soyayyanku tabbacin kuna tare dasu.

Waennan kananan kalmomi suna da muhimmanci matuka ga masoya duk jimawanku a soyayya ko rashin jimawa a soyayya , ko ta yaya yayin fadan kalmar “ina qaunar ka” yanada muhimmanci matuka,haka ma sauran kowanne yanada muhimmanci a cikin soyayyanku haka zalika akwai wasu kalmomi da suka kasance mata da maza suke sonji daga wajen masoyansu ko kaso kaji daga matarka ko kike so kiji daga wajen mijinki waennan kalmomi sune.

1) Nagode

Yin nuna godiya ga matarka ko mijinki a kowane lokacin da yayi ko tayi wani abu yana da matukar muhimmanci, kamar yadda yake da sauki yana kara karfafa dangantaka a kowane lokaci, wasu mutanen basa ganin bukatar godiya,suna ganin cewa Hakkin mazan ne suyi duk abinda ya dace a kansu, jinjinawa namiji yana sa soyayyanku ta bunkasa sosai.

2) Yi hakuri

Wannan kalma itace mafi girman kalma kuma haka zalika itace mafi girman kayan aiki wajen sassauta rikici tsakanin masoya, zai iya gyara wa ko kuma ya bata soyayya idan baa fadi yadda ya dace ba, mutum mai hikima shine wanda yake iya cewa yi hakuri a duk lokacin da sukayi kuskure, asalin shi ne kiyayewa da tabbatar da wanzuwar kauna da zaman lafiya.idan har kuna da wata daraja ga zamantakewarku to wannan kalma ba zai zama mai wuya a gareku ba idan zaku fada a lokacin da kuke bukatar nuna nadama kan laifin da kukayi haka zalika kuyi iya kokarinku don ganin hakan bata sake faruwa ba.

3) Ina goyon bayanki

Ka kasance tushen taimako ga matarka a koda yaushe ka kasance mai goyon bayanta a duk wani lamari,ka tabbata babu abinda baxaka iya ba a lokacinda matarka ta shiga wani damuwa.

4) Ina alfahari da kai

Ki kasance mai yin alfahari da masoyinki a koda yaushe,nuna masoyi ko masoyiywa nada muhimmanci a rayuwarki ko rayuwarka yana kara nisan soyayya a ko wane yanayi,musamman ga maza sun kasance suna son su jiyo kalmar ina alfahari da kai daga wajen matansu.

5) Ina qaunanki

Kalmar qauna kalma ce wacce bata gushewa a zuciya idan mutum yace ina qananki toh yana nufin soyayya ne na har abada, so da qauna akwai banbanci so yana iya kasancewa wani sifa na jiki mutum ya gani yake so, amma qauna yana nufin duk yadda mutum ya koma toh soyayyarka a zuciyanshi yana nan ba makawa.

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR