KAYAN GARGAJIYA GUDA BIYAR NA GYARAN JIKI

0
2267
Beautiful girl with curly hairstyle

Jikin mace da gyaran jiki abune dake fito da kyawun mace, yadda zaki kula da jikin  ki shine ki fitar da kyawun ki, yaka mata kowace mace ta kula da hakan. Abubuwa guda biyar da zakibi ki gyara jikin ki dasu.

      Man cocoa watau cocoa butter yana nan yellow ana samun shi a kwallon cocoa yana da matukar amfani a jiki, yana magance kyasbi da kuma bakaken tabo a jiki.Man cocoa yana hana layin jiki kuma yanasa jiki yayi kyau, yana da kyau a jiki  taimakawa  wajen   mmagance ciwo a fata diga ciki.

       Man kwakwa watau coconut oil ana amfani dashi a matsayin man shafawa, yana magance kyasbi da kuma cututukan yau da kullum na fata kuma yanasa jiki yayi tsantsi.

       Man kadai watau shea butter ana amfani dashi a gashi da kuma jiki. Yana sa jiki ya bushe. Man kadai zaa iya amfani dashi a matsayin abun gyara jiki ayi. Man kadai yana taimakawa fata diga rana kuma baya canza fata.

       Man kwakwan manja watau palm kernel oil, yana sa fata yayi laushi da sheki. Kuma yana magance gashi, yana sa gashi yayi kauri kuma yana rage karyewan gashi yana sashi yayi karfi.

       Sabulun salo watau black soap, magani ne ga kowane irin fata, koda fata mai laushi ne ko mai taushi, yana cire tabo a jiki kuma yana da kyau wajen cire kwalliyan fuska.

DAGA FAIZA A. GABDO