Yawancin iyaye a zamanin yanzu suna rainon ƴaƴan su da tunani mai tsauri wanda a ƙarshe yake sa su ga rayuwa a matsayin da bai kamata ba. Wani lokaci, yakan sa waɗannan yaran su ɗauki matakin da bai dace ba saboda tunanin da suka samu ta hanyar horarwa. a mafi yawan lokuta ba burinsu ba ne su tarbiyyantar da ’ya’yansu da munanan tunani da muradi. Yana iya zama dalilin irin tarbiyyar da suka samu su kansu, yana iya zama Saboda tsoro kuma yana iya zama wata hanyar kariya ne a wajansu. Koyaya, ba za a iya lamuntar wannan ba kuma. Dole ne kuma ya kamata iyaye su sani kuma su guje wa waɗannan kura-kurai yayin da suke renon yara.
- Tsananin duka
Yawancin iyaye suna aikata wannan kuskuren sosai. Wasu ma suna goyon bayan ayyukansu da aljanu. Ba daidai ba ne ku yi tunanin ɗanku yana da wani aljanu kuma za ku iya kubutar da shi ta hanyar dukan aljanin daga gare shi. Wani irin mahaukacin tunani!. Dukan yaron ba shine abu na farko da ya kamata ya fara zuwa zuciyarka ba ko da ya aikata wani abu da ba daidai ba komin muninsa. Ba wai muna cewa bai kamata a daki yaro ba amma bugun daya ko biyu ya isa. Shin kun gwada yin masu magana a hankali?. Zuciyar yara tana samun nasara ne ta hanyar zance na zuci da fahimtar juna ba ta bugun tsiya ba.
- Nisantar ra’ayoyinsu
Ko da yaushe ku kasance a buɗe da maraba don karɓar ra’ayoyi daga yaranku. Ko da ba ka hanzarta aiwatar da shi ba, yana sa su ji kai ne wanda za su iya magana da shi a ko da yaushe. Yin kuskuren guje wa kowane ɗan ra’ayi da suka kawo zai yi zama illa ne a gare su. zai iya sanya tsoro a cikin su, zai iya kawo rashin girman kai kuma yana iya sa su ƙi ku.
- Yanke masu hukunci
Kun sami damar yin rayuwar ku kuma ku zama duk abin da kuke so ku zama. Kada ku yi kuskuren tilasta wa yaranku wannan nauyi. Wasu iyaye a zamanin nan suna yanke shawarar abin da ’ya’yansu za su kasance kuma ba su ce komai ba a cikin al’amarin. Wannan mummunan abu ne kuma ba za a yarda da shi ba. Ya kamata a bar su su zama masu Ikon kansu tare da kuma mara masu baya a matsayin iyayensu. Kada ku yi kuskuren yanke shawarar rayuwarsu.
By: Firdausi Musa Dantsoho