Shin kun damu da dalilin da yasa fatar jikin ku take yadda take, bayan amfani da samfurin kula da fata masu kyau? Akwai lokutan da ayyukan yau da kullum na iya lalata mana fatan mu. Menene kurakurai na yau da kullun waɗanda zasu iya ƙara lalata mana fatan mu a karshe?
Na daya rashin kula da shimfidar gado da na matashin kai
Ko Sau nawa kuke amfani da shimfidar gado dana matashin kai don yin barci? Shimfidar gadon dana matashin kai yana da babban haɗarin tara ƙwayoyin cutar bacteriya idan ba ku kula da su ba yadda ya kamata.yayyin da fatar jikin ku ke hulɗa akai -akai tare da su, yana iya haifar da kamuwa da cutar fata watto infection.
Na biyu gujewa wanke fuska da safe
Wasu mutane ba sa wanke fuskar su bayan sun farka daga barci ko ma koma wanke hakorar su. Akwai tsarin nazarin halittu wanda ke faruwa lokacin da mutum yayi bacci wanda ya shafi gyaran fata. Wanke fuska da safe da kyau zai taimaka wajen wanke dattin da sebum, wanda zai iya haifar da kuraje a fuskar mu.
Na uku Yawan amfani da abun goge fuska watto face scrub
Kafin kuyi amfani da abun goge fuska, yakamata ku tuna waɗannan abubuwa guda biyu; kar ku yi amfani da shi da ƙarfi a fuskarku ma’ana durzawa kuma kada ku yi amfani da shi da yawa. Muna ba da shawarar ku yi amfani da shi sau ɗaya a mako idan kuna da bushashen fata watto Dry skin, yayin da masu fata mai maiko wato oily skin za su iya amfani dashi sau biyu zuwa uku a mako.
Na hudu Rashin Barci
Duk lokacin da ba ku sami isasshen bacci ba, kuna da alhakin samun kumburaren idanu watto eyes bag. Zai iya hanzarta nuna tsufan ku, ya ba ku yamutsheshen fata, ko sanya muku fata mara kyau. Yi wannan kyakkyawan barci kafin fata ta sha wahala daga rashin yin ta.
Na biyar Gujewa amfani da abubuwan kare fata daga hasken rana
Idan yanayi yayi zafi ko kuna son tafiya hutu zuwa wurin shakatawa ko rairayin bakin teku, abubuwan kariyan hasken rana zai taimaka muku kare fatarku daga wuce gona da iri ga hasken rana.
Yanzu da kuka koyi kurakurai na yau da kullun, Lokaci ya yi da za ku gano kurakuranku kuma ku yi abubuwa daidai kafin lokaci ya kure.
By Firdausi Musa Dantsoho