MATSALAN FYADE GA YARANMU LAIFIN UWA NE KO UBA?

0
254

 

 

A wannan zamanin an wayi gari cases na fyade ya kara yawa,Wanda hakan yana jawo kyama ga ya’ya mata. Da yawa daga cikinsu wannan matsala yana janyo musu tsangwama,kyama,kyantara wajen mutane musamman maza,sai ma kaji wasu suna alakanta ta da yar iska saboda dalilin an mata fyade, wasu suna iya cewa ma ita ta kai kanta idan har yarinya ta manyanta. Wannan matsala ya kan janyo da yawan mata su shiga cikin garari, wasu har makaranta sukan daina zuwa saboda tsangwama da kuma ta kura da suke samu daga wajen al’umma.

Ta yaya iyaye zaku kai hakkin dake bibiyarku?Domin kuwa hakkin yaranku a kanku yake musamman iyaye maza. Uba yana iya sati baiga yarsa ba amma bai san ya tabayi ina take ba, haka kuma ke uwa kin kasance kina barin yaranki kullum suna cikin yawo a unguwa, sune nan sune can ta yaya baza’a janyo miki yarki a lalata ta ba? Uba kai kasan bakada wadatan da zaka iya ciyarda iyalanka ba mai zai janyo haihuwa da yawa ko kuma aure aure? Saboda rashin abinci wani zai yaudari yarinya da minti ya kaita lungu ya lalata mata rayuwa shin ka mata adalci kuwa? Rashin kawota duniya a wajenta shi ne avu mafi dacewa saboda yadda aka lalata mata rayuwa.

Ya kai uba in har ka san bakada halin da zaka wadatar da iyalanka daina haihuwa shi ne abu mafi kyau agaresu domin alhaki ne a kanka duk abunda ya faru dasu. Ke kuma uwa yaranki musamman mata sune ya kamata kawayenki kuma abokan hiran ki , zuwa makwabta yin gulma ba naki bane in har kin haihu kusancin ki dasu shi zai hana yaranki fita yawo, kuma nuna musu gidan mahaifinsu shi ne gatansu shi zai hana su kwadayi har suji abun wani ya burge su.

 Haka zalika koyawa yaro ibadah da addu’a abune mai muhimmanci a garesu domin kuwa in har yaro yayi addu’a kafun ya fita toh duk wani abu da zai faru dashi a waje zai zo mishi da sauki. Da fatan iyaye zaku dauki darasi a daina batawa yaranku rayuwa.

Allah sa mu dace,Ameen.

BY:UMMUKHULTHUM ABDULKADIR