Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwa da Al’ummar Hausawa ke amfani dasu sosai a rayuwar su ta yau da kullum.Tana da amfani mai tarin yawa. Ana sarrafa tsamiya a matsayin kayan sha, inda a yau wajaje dadama wasu kan qullata a leda ko gora bayan sun taceta sun gaurayata da sukari sai su sakata a na’urar sanyi(refrigegrator) wadda ayau haka zamu koya maku.
Wasu kuma sun dauketa a matsayin magani da kuma sarrafata a matasyin abinci domin akan yi kunun tsamiya da kuma tuwon tsamiya a wasu yankunan arewacin nijeriya.
ABUBUWAN BUKATA:
*Tsamiya
*Citta
*Kaninfari
*Mazarkwaila ko siga
*Abarba
YADDA AKE HADAWA
- Da farko Ki jika tsamiyarki idan ya jiku sai ki juye a tukunya ki xuba citta d kaninfari ki tafasa sai ko tace idan ya huce.
- saiki markade abarban ki ki tace ki zuba a cikin lemun tsamiya.
3. Daga nan saiKi saka mazarkwaila ko siga ki gauraya sai ki saka a fridge yayyi sanyi asha lafiya.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho