Mashed potatoes abinci ne da yake da saukin hadawa kuma baya bukatan abubuwa hadawa masu yawa ko tsada, yawanci  abubuwan da ake hada shi das u abu ne wadda amarya da uwargida ba zasu rasa ba a cikin kitchen insu.
Shi wannan abincin baya daukan lokaci ga daddi ga kuma rike ciki.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
- Dankalin turawa
- Narkakken butter
- Gishiri
- Masoro
- Tafarnuwa
- Madaran ruwa
YADDA AKE HADA MASHED POTATOES
- Zamu fere dankalin mu sai mu yanka shi biyu daga tsakiya, daga nan mu sa a cikin ruwan da muka sa gishiri.
- Mu daura a wuta mu barshi yayi tausa kuma ya dahu ta yadda cokali mai yatsu watto fork zai iyya shiga ciki. Sai mu tsame a matsama.  Â
- Sai mu daura madaran ruwan mu a wuta ya danyi zafi, ba zafi sosai ba ya danyi lab- lab.
- Mu zuba dankalin mu daya dahu a kwanu sai mu sa butter a ciki mu motsa watto mashing. Sa’anan mu dinga sa madaran mu kadan-kadan muna motsawa da potato masher har sai komai ya hadu sosai.   Â
- Sai mu sa gishiri da tafarnuwa da masoro mu motsa. Toh mashed potatoes inmu ya hadu aci lafiya.
Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho