MUHIMMAN ABINCI DA YAKAMATA MU BAWA YARANMU DOMIN KAIFIN KWAKWALWA

0
568

 

Abincin dake kara kaifin basira a al’adance musamman a kasashenmu na hausa bamu cika baiwa yaranmu abinci da suke kara kaifin basira ba,iyaye sun kasance suna iyakan kokarinsu wajen ganin yaransu sunci abinci yadda ya kamata,sai dai matsalar ba kowace uwa bace tasan wadanne lafiyayyen abinci ya kamata yara su rika ci wanda zai taimaka musu wurin girman jikinsu da lafiyar kwakwalwarsu.A yawancin nau’in abinci da muke yawan basu shine carbohydrates wadda amfaninsa a jikin yaro shine ya kara masa karfi ne,wasu iyayen suna biyewa yaransu ta hanyar barinsu su zabi duk abinda suka ga dama wanda kila wannan abincin baida kyau wajen kara musu kaifin kwakwalwa. Yara suna bukatan duka wato;abinci mai gina jiki,abincin da zai kara musu karfi da kuma abincin da zai karawa kwakwalwarsu karfi domin cigaban rayuwarsu. Rashin baiwa yaro duka waennan sai kaga yaro ya taso yanada kuzari amma baida fahimta ko kaga yaro ya tashi yanada fahimta amma ba kuzari. 

 

A binciken wasu likitoci sun lissafo wasu abinci da zai kara taimakawa wajen kara kaifin kwakwalwan yaro, sunce rashin su ga yaro na iya saka yaro ya kasa fahimta ko kuma ya gane musamman wajen karatu. Ga sunan kamar haka;

1) Cin dafaffen kwai: wasu sun canfi baiwa yara kanana kwai kan cewa yaro idan ya yawaita cin kwai zai iya zamowa yaro mai halin bera,wannan canfi ne irin na bahaushe amma babu kamshin gaskiya a ciki. Don haka yakamata a dinga dafa kwai ana baiwa yaro a kalla a duk kwana biyu, sabida a cikin kwan ana samun wasu sinadarai da zasu taimakawa kwakwalwa da bada lafiyan jiki. 

2) Cin ganyayyeki: cin ganyayyeki kamansj karas,alaiyaho,tumatir da sauransu,Cin ganyayyeki: cin ganyayyeki kaman su karas,alaiyaho,tumatir da sauransu yana kara wa yara jini da lafiya . A koyawa yaro cin ganyayyeki ko bayaso domin shi yaro bai san abunda zai taimakesa ba, shi yaro yafi so yaci abincin da zaiji zaki ne kawai a bakinsa.

3) Kifi:A koyawa yaro cin kifi wadda wannan zaifi dacewa ne idan an yaye yaro a rika bashi kifi ko sau daya a sati,idan zaa baiwa yaro kifi a tabbata kifin ya soyu sosai sabida in har bai soyu sosai ba zai iya janyowa yaro tsutsan ciki.ko kuma a dafa shi ya dahu sosai kafun a bashi,zaka iya mishi paten dankali da kifi da alaiyyaho ka bashi.kifi ba iya kaifin kwakwalwa yake karawa yaro ba hatta karfin garkuwan jiki wato immunity yana karawa .

4) Madara: sai kuma madara musamman wadda aka rage kitse dake cikinta,madara na dauke da sinadarin vitamin B wadda yake taimakawa wajen bunkasa kwakwalwa, zaifi dacewa a sanyata misali in zaa baiwa yaro kamu sai a hada da madara a rika bashi tare in aka yawaita bawa yaro zallan madara yana iya kawo mishi basir wato kurga,amma idan har ana sanyata ne cikin wani abu a baiwa yaro toh bazata cutar da shi ba .

5) Shan zuma: A koyawa yaro shan zuma,yanada kyau a bawa yaro zuma mai kyau ba wanda akayi surki da suga ba, zaa ringa lasawa yaro ko sau daya a rana shima yana taimakawa wajen karawa yaro kaifin kwakwalwa.

6) Ruwan kwakwa: baiwa yaro kwakwa yana ci ko kuma yana shan ruwanta hakika har lafiyan ciki da jiki zata taimaka masa bama kwakwalwa kadai ba.

7) Cin kayayyakin lambu kamarsu abarba,kankana,lemu,ayaba da sauransu: abarba da ayaba suma suna daya daga cikin kayan lambu da suke taimakawa wajen kaifin kwakwalwar yaro.

8) Dabino: Abu na karshe shine dabino,baiwa yaro dabino yana taimakawa sosai wajen kara masa kaifin kwakwalwa musamman idan har anasi yana haddace Abu a take, don haka zaka iya baiwa yaro dabino a kalla guda daya ko wane rana musamman idan ya haura shekara 2 a duniya .

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR