Ruwan Shinkafa Don Gyara Gashi

0
554

 

Ruwan shinkafa ya na sa gashi kyau, ya na hana Shi tsinkewa da Kara mai tsawo saboda Rowan sitaci da ke ciki bayan an kwashe shinkafa. Ruwan shinkafa na da bitamin E, Amino Acid , bitamin B da ma’Dania masu yawn a ciki da kuma antioxidant.

Ruwan shinkafa shi ne wanan ruwan sitaci da ya rage bayan an tafasa shinkafa ko an jika na dan wani lokaci. Ruwan na sanya gashi sheki da taimakawa wajen girma da sauri.

Yadda ake yin ruwan shinkafa

● A samo shinkafa gwangwani daya
● A dauraye da ruwa sai a zuba mai ruwa da zai rufe shi don tafasawa ko kuma jikawa na minti 30

● A tace ruwan da kwando
● Sai a zuba ruwan a spray bottle don fesawa a gashi

Yadda za’a yi amfani da ruwan shinkafa

● Wanke gashi da shamfu
● A dauraye da ruwa sosai
● Sai a zuba ruwan a spray bottle a shafa a gashin
● Sai a tausa ruwan a gashi da fatar kai
● A bar shi na minti 20 zuwa 30
● A dauraye gashi da ruwan dumi

 

 

Safrat Gani