Fitacciyar jaruman finafinan hausa kuma tshohuwar matan jarumi sani danja mansurah isah tayi Allah wadai da irin kalaman da mutane keyi mata na suka domin ta fita daga gidan mijinta. A karon farko kenan da jarumar ta fito ta kuma maida wa wadanda ke sukarta martini inda take cewa maganganun da sukeyi na sukarta ya isa haka domin kuwa ba akanta aka fara saki ba.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta cewa; tayi hoton sallah ance abinda yasa ta fito kenan,tayi tafiya zuwa wani gari ance shiyasa ta kashe aurenta,taje cin abinci da kawayenta ance iskancin da take sonyi kenan,taje aikin NGO na rabo da ta sabayi sama da shekara 20 kenan tana wannan rabo ance daman yawon daya fito da ita kenan. Sa’annan jaruman tace saki ba haramun bane don manzon ALLAH ma yayi kuma shi muke koyi dashi. Mansura ta kuma cewa ba ita kadaice mai aure da aka fara saka ba, tace idan mutane sunga yayan masu kudi tsirara ko ba dankwali a kansu ba’a Magana sai dai a yabesu,amma in har yar film tayi wani abu sai a zageta,wannan ba adalci bane.
Tsohuwar jarumar ta kuma shawarci mutane da suji tsoron Allah domin daga yara har tsofaffi suna bibiyanta suna zaginta,tace su tambayi na kusa dasu yadda zafin saki yake suji domin sanin illar abinda suka mata. A karshe jaruman tace Allah zai saka mata,kuma bazata taba yafewa duk waenda suka shiga rayuwarta ba, Alla kuma ya jarabcesu da kuncin rayuwa na aure domin su gane kuskurensu.AMEEN YA ALLAH.
BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR