YADDA AKE HADA GAS MEAT

0
358

Abubuwan bukata sune:

 • Nama
 • Albasa
 • Bakin masoro
 • Gishiri
 • Kanunfari
 • Kuli2,
 • Ruwa kadan.
 • Tafarnuwa
 • Garin kuli-kuli
 • Man gyada
 • Garin yaji

Yadda ake hada gas meat

 1. Zaki yanka naman ki sala-sala sai ki samu sinadarin dandano, masoro,gishiri, garin yaji da tafarnuwa , ki zuba a cikin naman ki jujuya sai ki rufe ki barshi na minti talatin.
 2. Sai ki nemi tukunya ki zuba namanki da kikayi mai hadi a ciki, ki rufe har sai ruwan naman ya fara fitowa.
 3. Sai mu zuba yankake albasa,man gyada da garin yaji mu
 4. Sai ki zuba ruwa kadan ki rufe ya dahu na minti goma.
 5. Bayan minti goma sai mu zuba garin kuli-kuli muyi ta juyawa har sai ruwan naman ya tsose amma ba duka ba toh gas meat inki ya haddu.
 6. Kiyi serving da tumatur da albasa da dafaffen dankali.   

 

Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here