Yan fim mutani ne kamar kowa zasu iya yin kuskure a daina yin masu kallon yan iska. inji Hauwa Waraka

0
557

 

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai hausa  ta Kannywood, Hauwa Abubakar, wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta yi kira ga masu cewa yan fim musamman mata yan iska ne, da su daina yi musu irin wannan kallon, domin kuwa su ma mutane ne, kamar kowa za su iya yin kuskure kuma za su iya yin dai dai, don haka sai a rinka kallon su kamar sauran mutane in dai adalci a ke so a yi musu.jaridar dimokuradiyya na ruwaito.

Hauwa Waraka jarumace da  ta ke taka rawa a cikin yawancin fina-finan hausa da ta ke fitowa, musamman ma wadanda ta yi suna kuma ta fito a karuwanci da shu’ummanci, a hirar da akayi da ita wadda aka tambayeta game da rol in da take yawan fitowa ta bayyana cewa , “Ba hali na ba ne, yanayin rol din ne haka, kuma idan za a kalle ni a matsayin karuwa ai na fito a fina-finan da dama a wata siffar. Ka ga na fito a matar aure mai hakuri da biyayya ga mijin ta da iyayen ta, don haka fim ne ya ke zuwa da haka” inji ta.

Ta ciga ba da cewa, ” Amma yanzu da mu ke magana da kai a natse ka same ni, don haka rayuwar cikin fim daban, wadda mu ke yi a waje daban, domin a fim ana son a nuna fadakar wa ne, yadda mutane za su fahimci sakon, don haka masu kallon mu su gane abin da mu ke yi a fim rayuwar mu ba haka take ba”
A karshe ta ce, “Don haka a daina yi mana kallon ‘yan iska, don babu wanda ya ke so ya ga ya lalace ko wani na sa, don haka idan aka ga mun yi ba dai-dai ba, to a rinka yi mana addu’a ta alheri, ta haka ne za mu gyaru.

Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho