Creamy chicken soup miya ne da yake da saukin hadawa ga daddi kuma baya bukatan kasha kudi domin hadasa.
Shi wannan miyan yana da daddin sha zallan shi musamman a wannan lokacin sanyi ana kuma iya hada shi da farar shinkafa,farar taliya ko macroni.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
- Zallan tsokan kirgin kaza
- Karas
- Peas
- Green beans
- Masaran gwangwani
- Butter
- Flawa
- Madaran ruwa
- Sinadaran dandano
- Ganyen celery
- Gishiri
YADDA AKE HADA MIYAN
- Zamu yanka tsokan kirjin kazan mu kanana sai mu zuba gishiri da sinadarin dandano mu tafasa.
- A wani tukunya mu sa butter idan ya narke sai mu zuba karas,peas da masaran gwangwani mu a ciki mu dan soya,
- Sai mu zuba flawa mu aciki mu juya zamu gan cewa flawan ya kama jikin suk karas in kuma ya shanye butter in.
- Sai mu zuba ruwan madaran mu mu juya,sai mu dauko ruwan da muka tafasa kazan mu mu kara aciki.
- Sai mu zuba tsokan kazan mu, sinadaran dandano, ganyen celery,garin tafarnuwa,garin citta,da masoro mu juya sai mu barshi na minti 3.
- Bayan minti uku creamy chicken soup inmu ya hadu. Asha lafiya
By: Firdausi Musa Dantsoho