Gashi wani bangare ne na jiki karkashin fata da ake kira gashin follicle wato hair follicle, ko kuma idan aka ja daga fatar ya fita. Wanan sashin jiki yana bukatar kula na massaman.
Ko gashi na zubewa ana iya amfani da abubuwan da suka dace don sa gashi tsawo da hanashi tsinkewa, ana gyaran gashi da abubuwa da za su sa gashi laushi da danshi wato moisture don hanashi tsinkewa da sa shi tsawo.
Ga abubuwan da ake bukata don turara gashi (steaming)
1. Ababa day a ko biyu
2. Farin kwoi (egg white)
3. Vitamin E
4. Yoghurt
A fasa kwoi a yar roba, a bare ayaba daya, a saka vitamin E sai a zuba yogurt chokalin cin abinci biyu a makarda da abun nikan turawa blender.
A wanke gashi tsaf sai ki ki shafa wanan hadin na tsawon minti 30 zuwa hour daya sanan ki dauraye gashin da ruwan dumi, sai ki kitsa yadda kike so.
Za ki iya yi duc wata kokuma sati biyu-biyu.
Safrat Gani