Yadda zamu turara fuskan mu

0
116

Turara fuska yana buɗe kofofin ku, yana yin abubuwa waɗanda ke toshe ramukan don a samu cire su cikin sauƙi. Turara fuska shima yana taimakawa wajen sarrafa mai kuma yana saka fuska kyalli sosai, musamman idan anyi amfani da abin rufe fuska mai kyau da abun mutsuka fuska.

YADDA AKE TURARA FUSKA.
1. A samu kwanon ruwan zafi mai tururi
2. A sa mai kadan ( Rose ko lavender mai me muhimmanci)
3. Ku samu zani ko tawul ku rufe kanku a kwano
4. Ku bari tururi ya dumama fuskarku na kusan mintuna 10.
5. Sai ku wanke da ruwan sanyi.

Ku rinka turarawa sau daya a mako, yakamata a yi amfani da sabulu abun goge fuska nan da nan bayan fuska mai tururi, saboda hakan yana sauƙaƙe cire matattun ƙwayoyin cuta da ƙazanta waɗanda fuskar ta taso.

Haka ma zaku iya amfani da abin rufe fuska na gawayi a fuskarku sannan ku mutsuka  fuskan ku idan kun gama.

Daga Faiza A.gabdo