Fata yana bukatar kulawa mai yawa idan har Mutum na son ganin sakamako mai kyau a fatan sa. Wannan shine dalilin da ya sa ayau a cikin shirin mu na kwalliya zamani zamu kawo maku manyan abinci guda goma waɗanda suke da muhimmanci ga fatan mu don samun kyakkyawan fata da kuma fata mai sheki wanda duk muke nema!
- Kifin Salmon
Kifin Salmon yana da wadatan antioxidants a cikinsa ya kuma mallaki kitse na fatty acid a cikinsa mai yawa wanda shine dalilin da yasa yake cikin manyan abinci goma da zasu iya amfanar fatan mu. Tunda fatar jikinmu ba zata iya samar da waɗannan acid mai kitse ba, shi ya sa cin su na iya taimakawa fatarmu sosai. Cin kofin salmon na iya kwantar da kumburin da zai iya bayyana a fatar jikin mutum, ya jaddada A takaice dai, suna kulle danshi da ake buƙata a cikin fata yayin tabbatar da cewa babu wani abin da zai bata wa mutum fatansa mai laushi. Idan kuna fuskantar matsalar fata to yakamata ku yawaita cin kifin salmon!
- Kankana
Mun san cewa wannan na iya zama kamar rashin tunani, amma, an tabbatar da cewa wannan hanyar tana aiki! Idan kun fuskanci kumburi a idanunku ko ko’ina a fuskarku, to cin kankana yana taimakawa wajan magance wannan matsalar. Tarruwan Ruwa a fuska yana haifar da kumburi a fuskar mutum kuma tunda kankana yana dauke da yawan ruwa a cikinsa, zai iya rage kumburin fuskar. Baya ga hakan, kankana, idan aka kwatanta da sauran ‘ya’yan itacen, yana da ƙarancin sukari don haka bai kamata ku damu da yamutsewar fatar ku wadda zai bayyana a farkon matakin rayuwar ku ba! Tare da kankana, za ku rage kowane nau’in kumburi da kumburin fuska wanda zai iya bayyana akan fata mutum mai taushi!
- Tumatir
Sanya mai mai kare fata daga kunar rana na da gajiyarwa. Sanya samfurin da zai iya kare fata mai laushi daga kunar rana masu cutarwa na iya zama ƙarin mataki a cikin tsarin kula da fata, don haka maimakon amfani da shi samfurin za mu iya zaɓar samfuri da zamu ci! Haka ne, tunda tumatir yana da dauke babban sinadari a cikisa na lycopene, wannan yana nufin cewa a zahiri yana da fa’ida ga fatar ku kuma yana iya kare mana fatan mu daga hasken rana. Ko dayake, mun fahimci ba kowane ke son cin tumatir ba shi ya sa muke tattare da abinci iri iri kuma wanda za ku iya ci a madadin abinci wanda zai iya amfanar da fata iri ɗaya dana tumatir. Sauran abincin da ke da sinadarin na lycopene a ciki shine kankana, innibi, da gwanda. Don haka, kada a sami uzuri don rashin cin abinci mai ɗauke da sinadarin lycopenes !
4.Karas
Idan kuna fuskantar yawaitar mai a fatar ku kuma a sakamakon haka, kuna kuma ganin kuraje sun bayyana, to hanyar da za a magance wannan matsalar ita ce ta hanyan cin ɗanyen karas a kowace rana, waɗanda ke ɗaya daga cikin abincin da za su iya amfanar fatar mu. hanyoyi daban -daban. Karas suna da babban sinadarin beta-carotene, wanda shi ne farkon sinadarin Vitamin A wanda kuma ya kasance babban sinadarin Retina-A. A cikin kalmomi mafi sauƙi, kuna buƙatar neman wannan bitamin idan kuna son rage ƙimar mai a fatan ku. Idan kun kasance masu fata mai maiko, to ku tabbata ku duba wasu samfuran fuska waɗanda ke tattare da waɗannan bitamin, ko, kuma ku dinga taimaka wa fatan ku ta hanyar cin karas.
- Avocados watto pear
Ana iya samun watto Avocados watto pear kusan a ko’ina a kwanakin nan. Amma dalilin da yasa ake yawaitan neman pear shine galibi saboda amfaninsa , da kuma cewa suna ɗaya daga cikin abincin da zai iya amfanar fata mu. Wato, su na da babban sinadarin da ke face mask na gyaran fuska da saboda su na ɗauke da bitamin A, D, da E tare da kyawawan kitse. Idan kuna son ba wa fatan ku cikakkiyar haske mai lafiya to za ku iya cin sa a matsayin abinci ku kuma kuyi amfani da shi a matsayin abin gyaran fuska watto face mask! Muhimman bitamin da fats watto kitse masu kyau za su shiga cikin sel na fata zuwa mafi zurfi kuma ta haka ne za su ba da sakamakon da kuka dade kuna nema wa fatanku. Yin Amfani da pear zai gyara maku fatan ku sosai!
- Lemu watto oranges
An gudanar da gagarumin bincike dangane da fa’idar lemu, wanda yana daya daga cikin manyan abinci da zasu iya amfanar fatar mu. Dangane da Jaridar American Journal of Clinical Research, an tabbatar da cewa lemu yana da babban sinadari a ciki na bitamin C. Bitamin C yana da fa’ida ga fata idan kuna son hana bushewar fata da yamutsewar sa. Sauran abinci irin su innabi, strawberries, da barkono ja na iya taimaka wa fata sosai idan lemu ba taku ba ce ma’ana ku ba ma’abotan Shan lemu bane. Don haka dole ne ku sha lemu, musamman idan kuna son dakatar da bushewar fata a cikin watanni lokacin sanyi! Wataƙila ba za ku ga waɗannan sakamakon nan take ba, amma ku kasance a shirye don waɗannan sakamako na dogon lokaci!
7.ganyen Kale
ganyen Kale abinci ne wanda ke ɗauke da yawan bitamin A wanda shine babban sinadarin Retina-A, magani da ake amfani da shi don warkar da kuraje. Idan kuraje wani abu ne da kuke gwagwarmaya da shi to muna ba da shawarar ku cinye wasu ganyen kale wanda shine mafi kyawun yanayi kuma mai daɗi don kawar da wannan kurajen da ba a so. Hakanan ana amfani dashi don magance duk wani rauni, tabo, da kuraje idan an shafa shi a fata. Don haka idan kun sami kuraje ko dai tabo a matsayin matsala, to yakamata ku gwada Kale domin kawar da matsalan. ZaKu iya Gwada haɗa shi cikin salads ɗin ku, ko sandwiches, ko kuma kuna iya ci sa kai tsaye!
8.Almonds
Almonds suna da wadattacen bitamin E a ciki, wanda shine antioxidant mai ƙarfi wanda ke taimakawa hana bushewar fata, yamutsewar fata, da kuma kansar fata! Wannan daidai ku ne, akwai wasu fa’idodi da yawa daga cin ɗan yatsan almond. Ba za ku tabba damuwa da yanayin fatar ku, da ma lafiyar fatar ku gaba ɗaya ba. Dole ne ku kula da fata ku kuma cin almond guda biyu a kowace rana zai bawa fatar ku kulawa da yake bukata!
9.Chocolate mai duhu watto dark chocolate
Chocolate na iya yin abubuwan al’ajabi da yawa ga fatar mu. Dark cakulan yana da kyau wajan karfafa mana fatanmu. Ko da yake mu tabbatar idan zamu ci cakulat ya kasance wanda ke da cacao kashi 70 ko fiye da haka a cikinta, saboda duk wani chocolate da ke da kasa da kashi 70 na cocoa yana ƙunshe da sukari mai yawa wanda zai iya lalata fata kuma yana ƙara haɓaka yamutsewar fata da wuri. Mu Tabbatar mu karanta abin da chocolate ke kunshe da shi kafin mu fara cinsa.
- Wake watto kidney beans
Waken kidney beans yana da yawan sinadarin zinc kuma wannan shine ainihin abin da kuke buƙata don yaƙar kurajen ku! Waɗannan wake suna da yawa kuma za ku iya amfani dasu a kowane abinci da za ku dafa. Zai yaƙi kurajen da ke fatanku, yayin da yake ba ku babban tushin furotin don baku fata mai ban mamaki.
By: Firdausi Musa Dantsoho