Soyayya da Shakuwa

0
625
Mutane da dama basa iya bambancewa tsakanin Soyayya da shakuwa domin sukan ajiye soyayya a matsayin  shakuwa.
Menene shakuwa?
Ana samun shakuwa a abota ko Kuma kawance, domin mutanen da suka shaku zaka samu komai nasu Yana iya zama daya hatta ra’ayi, daya baya iya daukan lokaci mai tsawo ba tare da yaga daya ba sannan idan suna Hira har basa son rabewa, hatta laifi daya baya son na daya, akwai kamaceceniya tsakanin Soyayya da shakuwa musamman ga mace da namiji. Hakan yake sa idan shakuwa tayi shakuwa Mai ra’ayin soyayya tsakani zai dinga ji a ranshi kamar suna son juna ne harma ya kai ga gwadaya ta hanyar sanar da dayan cewa Yana so. Akasari idan haka ya faru wanda akace ana so zakaga ya fara janye jiki ,hakan yana nufin Yana so ya fahimtar da dan uwan shi shakuwa ce fa ba Soyayya ba domin ita Soyayya idan ta Kama zuciya, wani sabon yanayi mutum yake ji na daban zai dinga jin kamar ya fada cikin wata sabuwar duniya ce ta daban.
Ga mutanen suka shaku, sukan iya hirar su, idan suka gama kowa yaje yayi barcin shi kashe gari idan aka farka kowa ya gama harkan dake gaban shi kafin su nemi juna Kuma don suyi hira ko kuma suga juna.
Ana fahimtar akwai so Bayan anshaku ne ta wasu hanyoyi dake bambanta tsakanin so da shakuwa. Yanayi mafi Dadi shine yayinda mutum ya samu so yayin shakuwa domin babu soyayyar da tafi Dadi duniya sama da soyayyar da ta hada da shakuwa domin ana shakuwa babu so kamar yanda ake so babu shakuwa, misalin so babu shakuwa yana da yawa domin ga ma’abota Soyayya sun sani, musamman ga diya mace ,kai har da namijin ma, wata/wani kan iya dakon soyayyar a zuciyar harna tsawon lokaci ,wani ma har ya mutu ba tare da ya sanar da wanda yake so ba ko ince ba tare da ko gaisawa ya tabayi ga Wanda yake so ba.
Mafi dadin alaka itace Soyayya da shakuwa. Ya ake gane Bayan Shakuwa akwai So? Yayin da saurayi da budurwa suka shaku suke muradin ganin juna, suke jin dadin hira da juna, sannan basa gajiya da zama tare da juna ko Kuma nace da hira da juna. Duk wannan abubuwan da na lissafo suna wakana yayin shakuwa, Amma da zarar bayan kun rabu da juna zaku fara tunanin juna, zakaga yayin tuna juna mutum yana murmushin da shi kanshi baisan dalili ba wani sa’ilin har ma dariya. Idan ka kwanta ka tashi zaka fara lalubar waya domin kaga ko ankira,  idan ba’a Kira ba kai ka Kira, yayin da kaga anfara kaci abinci ko me kikeyi toh ko shakka babu an rikide shakuwa xuwa Soyayya. 
Wannan shi ake Kira da Soyayya da shakuwa. Mu sani cewar So da shakuwa kowanne zaman kan shi yakeyi sai dai kowanne kan iya faruwa bayan daya ya faru, ma’ana ana cikin Soyayya shakuwa na shiga ciki kamar yanda yayin shakuwa akan iya kamuwa da Soyayya ,sannan Kuma masoyan da suka hada Soyayya da shakuwa sune masoyan da suka fi jin dadin alaqar su, domin sune masoyan da zaka samu basu cika samun matsala a soyayyar su ba.
Daga Maryam Idris.