DUK ZAMAN DA ZAMUYI DA HUKUMAR HISBAH BA ZAI ZAMA MAFITA BA A WAJEN TSAFTACE FINA-FINAI -Tahir Fagge

0
65
Fitaccen Jarumin masana’antar  ta kannywood Tahir Muhammad Fagge Wanda aka fi sani da Tahir Fagge ya bayyana cewa kalubalen da Masana antarsu ke fuska, ba sabon al amari bane a wajensu,domin tuntuni suke tsabtace masanaantar ta yadda zatai daidai da al adar malam bahaushe . Tahir din ya bayyana hakane ta cikin shirin KANNYWOOD A YAU NA GIDAN TALABIJIN DIN TOZALI. Inda ya kara da cewa tun kafa Masana’antar suke kokarin tsabtace masanaantar ta hanyoyi daban – daban tare da   masu aiki a karkashin Masana’antarsu.
     Tahir Fagge ya bayyana goyan bayansa ga ya yadda Gwamnatin Jihar ta kano ta ke damuwa da Sha anin masana’antar, sai dai yace malamai ne yakamata su gyara tsarin  da suke so masana’antar ta kasance ,ta hanyar daukan nauyin Sha anin masana’antar, Sannan Suzo a dama dasu a kowanne gaba a cikin harkar fim din duba da céwa koda sun daina kannywood din to akwai sauran takwarorinsu na masana’antu nishadantar wa, wadanda suka haɗar da masana’antar kudancin Najeriya wato Nollywood ga kuma masana’antar kasar Indiya wato Bollywood sannan da masana’antar kasashen waje Hollywood, kuma duk al ummarmu na kallonsu .
A cewar sa Idan Al umma ba su karbi dan halaq ba, to yaza ayi da wadancan masana’antun? Kuma duk Al ummarmu na kallonsu. A karshe dai Tahir Fagge yayi cikakken bayanin haryoyin da yakamata a tsabtace masanaantar. Cikakken tattaunawar zaizo muku ta cikin shirin KANNYWOOD A YAU da zamu haska muka a wannan makon Wanda yake zuwar muku a duk ranar Jumaa da misalin karfe 6:30 na yamman sannan mu maimata muku shi a duk ranar Asabar da misalin karfe 10:30pm.
KADAN DAGA CIKIN  MAGANGANUNSA AKWAI👇
 Hanyoyin da malaman kiristoci ke bi wato kungiyar CAN suke bi wajen tallafawa masu harkar fina -finan a yankunan su . Tare da yada daawar addininsu ta hanyar Yan film, bawai yana nufin malaman mu suyi koyi dasu ba sai dai akwai dabaru da yakamata abi,wadannan dama wasu bayanai NA cikin shirin .
HAFSAT IBRAHIM