Har hana mu yin sana’ar fim akayi amma hakan bai sa na sauya Jam’iyya ba tun da na fara siyasa – Sani Danja

0
368

Fitaccen Jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannaywood, Sani Musa Danja wadda akafi sanni a sani danja ya ce, ya tsaya a Jam’iyyar guda watto PDP, ba ya bin wasu ‘yan siyasa, kamar yadda wasu ‘yan masana’antar fina-finan hausa ke yi.

A ranar laraba ne fitaccen jarumin ya bayyana hakan a wanni shiri da akayi dashi a gidan rediyon dala.

Jarumin ya bayyana cewa , Har shan ruwa wasu ‘yan siyasar sun taba gayyatan shi, amma wannan bai ja hankali sa ya bar Jam’iyyar PDP ba har yanzu yana cikin ta”.

Ya kuma cewa, ya fuskanci kalubali kama daga rufe masa shago zuwa  hana shi yin sana’ar Film a Kano, amma hakan bai sa ya sauya Jam’iyya ba kuma yana nan a inda aka san shi watto jam’iyyar PDP. Inji Sani Danja

Sani Danja ya kuma kara da cewa, nan gaba kadan za a ji matsayar su a siyasa, amma kawo wannan lokaci ya na nan a Jam’iyyar PDP har yanzu.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho