JARUMI ALI NUHU YA CIKA SHEKARU 47 JARUMAI KANNYWOOD SUN TAYA SHI MURNA AMMA BANDA RAHMA SADAU DA SADIQ SANI SADIQ

0
546

Fittacce  kuma shaharraren jarumin Kannywood da nollywood ali nuhu wadda akafi sani da sarki ali nuhu ko sarki ya cika shekara arba’in da bakwai 47 a duniya a ranar 15 ga watan maris shekara ta 2021 wanda a ranar kafafen sada zumunta ya cika da masu taya sa murna.

Domin taya sa murna masoyansa abokanayan aikin da ma manya manyan jaruman Kannywood wanda ke  kusa da jarumin sun taya sa murnar cika shekaru 47.

Amma abun da ya jawo hankalin mu game da wannan ranar shine rashin ganin jaruma rahma sadau da jarumi sadiq sani sadiq sun taya sarki ali nuhu murna a wannan babban ranan.

Zamu iya ce jaruma rahma sadau na da hujan rashin taya sa murna saboda a ranar cika nata shekaran jarumi ali nuhu bai taya ta murna ba, hasali ma jaruman basa bin junansu a shafuka na sada zumunta wadda hakan ya fara ne tun bayyan bayanan hoton jaruma rahma sadau da ya janyo har aka taba martaban manzon Allah, kuma jarumi ali nuhu ya bayyana rashin goyan baya ga jaruman a wannan lokaci wanda mu ke kyautata zaton shine dalilin rashin jituwan su.

Amma shi kuma sadiq sani sadiq babu wata takammaiman abu da za,a ce ya hada shi da jarumin amma za,a iya ce rashin jituwansu ya fara ne tun shekaran da ta gabata domin jarumi sadiq sani sadiq bai taya sa murna ba a shekaran da ya gabata ko da yake shima jarumi ali nuhu bai taya sa murna ba a ranar cika shekaransa amma ya taya murnar cika shekara bakwai da aurar matarsa.

Hakazalika jaruman biyu sun rage sanya hotunan juna a shafukansu na sada zumunta, ko da yake, an fara fahimtar rashin jituwansu ne tun a shkara ta 2020 inda jarumi sadiq sani sadiq ya bayyan cewa bashi da uban gida a Kannywood yayyin da jarumi ali nuhu yake daya daga cikin waenda suka fitar da jarumin a Kannywood musamman ma da fin insa mai suna ADAMSY.

Muna fatan Allah ya hada kawunan su.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho