Najeriya na da yan wasan da za su lashe gasar AFCON inji Mohamed Salah

0
81

Kyaftin din kasar Masar Mohamed Salah ya bayyana ra’ayinsa game da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya gabanin wasansu na farko na rukuni a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).

Ana sa ran dan wasan mai shekaru 29 zai jagoranci Masar da Super Eagles a fafatawar da za ta kasance muhimmiyar kungiyar da ta zo ta daya a rukunin D.

 

A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu, 2022, dan wasan na Masar ya bayyana cewa Super Eagles na da abin da ya kamata ta dauka domin daukaka kofin AFCON2021.

Ya ce, “Najeriya na da ‘yan wasan da za su iya lashe gasar, ni dan wasa daya ne a kungiyar ta, ba na daukar tambayoyi da ra’ayin kaina, suna da ‘yan wasa masu kyau, amma za mu yi iya kokarinmu don samun nasara a gobe.”

 

Daga nan Salah ya ci gaba da bayyana burinsa na jagorantar kasar Masar ta lashe gasar AFCON karo na takwas.

Ya ce, “Zan so in lashe wani abu tare da kasar kuma zan ba da mafi kyawun kwarewa ga kungiyar, muna da koci da ‘yan wasa nagari kuma da fatan za mu ci nasara.

Da aka tambaye shi game da barazanar da yake yiwa sauran kungiyoyi a gasar, Salah ya bayyana cewa yana son yin fice ne a rukunin.

Ya kara da cewa “Ni dai ina cikin kungiyar kuma ba zan dauki kaina a matsayin dan wasan da ya fi kowa iyawa a kungiyar ba, na zo ne domin buga wasa da kungiyar.”

 

Da yake tattaunawa kan kalaman da Jurgen Klopp ya yi masu cike da cece-kuce game da gasar cin kofin Afrika, Salah ya kare manajan kulob din.

 

“Klopp yana fadin hakan a matsayin wasa, yana son mu zo. Ya gaya min, yana fatan in yi nasara, ban san abin da ya gaya wa Mane ba. A Ingila, suna daukar AFCON a matsayin babbar gasa.”

 

Salah da Masar za su kece raini da Super Eagles a wasansu na farko na rukunin D da za a yi ayau 11 ga watan janairu 2022 a Garoua.

By: Firdausi Musa Dantsoho