Ayau, zamu kawo maku yadda ake hadda lemu mai daddi da saukin haddawa.shi wannan lemun babu giya a ciki ko kadan kuma zamuyi amfanin da iyayan itace wadda suke da amfanin ga jikin dan adam.
Abubuwan bukata sune:
- Abarba
- Madaran kwakwa watto coconut milk
- Lemun abarba
- Siga
- kankara
yadda ake hada pina colada
- zaki zamu blender inki mai karfi wadda zai iyya jure wahala sai ki zuba abarban ki mai kankara.
- Bayan kin zuba abarbanki sai ki sa kankara, madaran kwakwanki,lemun abarba da siga ki nika su gabaki daya.
- Toh lemunki ya hadu sai ki samu kofin ki, ki zubz a ciki kasha da sanyin sa.
Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho