Abubuwan Bukata Sune:
- Dankalin turawa
- Nikakken nama
- Attaruhu
- Thyme
- Curry
- Tafarnuwa
- Citta
- Sinadarin dandano
- Gishiri
- Man gyada
- Albasa
Yadda Ake Hadawa
- Da farko zamu fere dankalin mu,sai mu zuba acikin tukunya, mu sa gishiri da ruwa mu dafa.
- A wani tukunyan suya daban, mu sa man gyadan mu idan yayyi zafi sai mu zuba albasa da nikakken naman mu.
- Bayan mun sa naman mu sai muyi ta juyawa har sai yayyi kalar dahuwa sai mu sa nikakken attaruhu,curry, thyme,citta da tafarnuwa mu juya.
- Sai mu sa sinadarin dandanon, mu juya har sai ya dahu.
- Bayan naman mu ya dahu sai mu dauko dafaffen dankalin mu, mu murmusa watto mashing in shi.
- Mu zuba naman, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin dandano,curry, thyme a cikin dankalin mu juya su hadu.
- ki shafa man gyada a hannun, sai ki dibo hadin dankalin sai ki mulmula.
- Bayan kin gama mulmulawa, ki fasa kwai a wani kwanu daban sai ki sa man suyan ki a wuta yayyi zafi.
- Idan man ki yayyi zafi sai ki dauko dankalin kid a kika mulmula ki sa a cikin kwai sai ki jefa a cikin man kid a yayyi zafi.
- Haka zaki yi har sai kin gama soya duka dankalinki.
- Meat potatoe balls ya hadu a ci lafiya.
Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho