Hadin tafarnuwa da citta watto ginger and garlic paste hadi ne da keda amfani sosai wajan girki, wasu na amfani da waenan sinadaran kamshi da dandano a kowani girkin su.
Wanan hadin na iya yiwa mutun wata daya ba tare da ya bace ba, kuma yana kawo saukin bare tafarnuwa da citta a kullum.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
- Tafarnuwa kofi biyu
- Citta kofi daya
- Man gyada cokali shida
YADDA AKE HADAWA
- Zamu bare tafarnuwan mu da citta.
- Mu yanka tafarnuwan mu da citta kanana.
- Sai mu zuba su a cikin blender inmu da man gyadan mu, sai mu nikka yayyi laushi.
- Idan yayyi laushi toh hadin tafarnuwan mu da citta yayyi.
- Mu samu kwalba mai murfi mu zuba a ciki mu sa a cikin fridge .
ABUN LURA: zamu iya anfani da wanan hadin a dafa dukan shinkafa, tafasan naman mu, miyan kuka da ma abinci da yawa domin kara masa daddi da dandano.
Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho