Gwaje-gwajen kiwon lafiya guda hudu da yakamata masu shirin yin aure suyi kafin aure.

0
323

Aure alkawari ne na rayuwa wanda yakamata a dauki shi da mahimmanci. Lokacin da masoya suka yi aure ba tare da sanin yanayin lafiyarsu ba, yana iya haifar da matsala daga baya. Don haka yana da mahimmanci ku san tarihin lafiyar ku da na abokin tarayyar ku kafin ku yi aure.

Ga wasu ‘yan gwaje-gwaje da yakamata kuyi la’akari dasu kafin kuyi aure.

CUTAR KANJAMAU

Kafin ku yi aure, yana da mahimmanci ke da wadda zaki aura ku san matsayin ku na cutar kanjamau . Domin ana iya daukar kwayar cutar ta hanyar jima’i da ma wasu hanyoyi da dama, yana da matukar muhimmanci bangarorin biyu su tabbatar sun basa dauke da cutar. Hakanan yana da mahimmanci a duba yiwuwar kamuwa da wasu cututtuka na rayuwa kamar Hepatitis B da C da Herpes, da kuma wadanda za a iya warkewa kamar gonorrhea, syphilis, kwayoyin vaginosis, ciwon yisti, chlamydia da sauran su.

GWAJIN HAIHUWA

Mutane da yawa sun yi aure tare da fatan wata rana su zama iyaye. Waɗannan muradin na iya rushewa idan ɗayan biyun na da matsalar rashin haihuwa. Don haka yana da mahimmanci ga masu niyyar yin aure da suyi la’akari da yin gwajin haihuwa don gujewa halin da ake ciki na nadama da kuma abin da ke tattare da shi.

Gwaje-gwajen haihuwa sun hada seminal analysis, hormonal assay; pelvic ultrasound scans don sanin yanayin gabobin haihuwa na ciki da sauransu.

GWAJIN GENOTYPE

Wannan wani muhimmin gwaji ne da ya kamata masu shirin yin aure su yi musamman mutanen Afirka don gujewa haihuwar yara masu cutar sikila.

Cutar tana faruwa ne lokacin da iyaye biyu ke ɗauke da sifar sikila. Cutar na rayuwa kuma tana haifar da rashin lafiya mai tsanani. Idan an gwada ku kuma ya kasance kuna ɗauke da sikila, dole ne ku guji auren abokin tarayya wanda kuma ke ɗauke da sikila ko kuma wanda hadin ku na iya haifar da da mai dauke da sikila.

GWAJIN RUKUNIN JINI WATTO BLOOD GROUP

Mutane da yawa yawanci suna la’akari da mahimmancin gwaje-gwajen genotype amma sun kasa fahimtar cewa gwajin rukunin jini shima yana da mahimmancin . Gwajin rukunin jini ba kawai yana da mahimmanci ne a lokacin da a aka buƙaci ƙarin jini ba, yana da mahimmanci a guje wa batutuwan da matsalolin kiwon lafiya da suka shafi rukinin jini irinsu Rhesus factor.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho